DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeKasuwanciIMF ta ba Nijeriya shawarar ƙara haraji kan fetur da sadarwa

IMF ta ba Nijeriya shawarar ƙara haraji kan fetur da sadarwa

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya ba gwamnatin Nijeriya shawarar ta fara ɗora haraji kan kayayyakin man fetur da kuma ayyukan sadarwa domin ƙara kuɗaɗen shiga da kuma samar da isassun kuɗaɗe don ayyukan ci gaba da tallafa wa al’umma.

IMF ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na 2026 kan tattalin arzikin Nijeriya, inda ta ce duk da sabbin sauye-sauyen haraji da aka yi a ƙasar, har yanzu ana buƙatar ƙarin matakan tara kuɗaɗen shiga a shekaru masu zuwa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa IMF ta kuma ba da shawarar ƙara harajin VAT, faɗaɗa VAT zuwa kayayyakin man fetur, rage wasu keɓantattun haraji da kuma ƙaddamar da haraji a fannin sadarwa. Sai dai asusun ya yi gargadin cewa dole ne a yi la’akari da matsalar talauci da ƙarancin abinci kafin aiwatar da irin waɗannan matakai.

Rahoton ya nuna cewa sabbin manufofin harajin za su iya ƙara wa gwamnati kuɗaɗen shiga da suka kai kashi 3.9 cikin 100 na tattalin arzikin ƙasa cikin shekaru uku. Haka kuma IMF ta ce inganta tsarin tattara haraji da amfani da fasahar zamani wajen bin diddigin masu biyan haraji na iya ƙara samar da wasu kuɗaɗen shiga masu yawa.

Sai dai ƙungiyoyin ma’aikata da masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa sun sha nuna adawa da irin waɗannan haraje a baya, suna masu cewa ƙarin kuɗin zai iya jefa al’umma cikin ƙarin tsadar rayuwa ta hanyar ƙara kuɗin kira, bayanan intanet da kuma farashin sufuri da kayan masarufi.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata