DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiMun ji zafin rasuwar Manjo Janar Rabe mai ritaya - Hedikwatar Tsaro

Mun ji zafin rasuwar Manjo Janar Rabe mai ritaya – Hedikwatar Tsaro

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta ce ta yi baƙin ciki da alhinin kan rasuwar tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Soji, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu bayan ya shafe lokaci a hannun masu garkuwa da mutane.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce rasuwar marigayin babban rashi ne ga rundunar soji da kuma ƙasar baki ɗaya.

Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa ta guji yin tsokaci a bainar jama’a kan sace Manjo Janar Rabe Abubakar ne domin ba wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukan ceto ba tare da tangarda ba.

A cewar rundunar, jami’an tsaro sun yi amfani da dukkan kayan aiki da dabarun da suke da su wajen ƙoƙarin ceto marigayin tare da dawo da shi gida lafiya, amma abin takaici hakan bai samu ba.

Sai dai rundunar ta ce wannan lamari ya ƙara mata ƙwarin gwiwa wajen tsananta hare-hare da ayyukan sintiri kan masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a faɗin Nijeriya.

Hedikwatar Tsaro ta kuma yi alƙawarin ci gaba da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kamo waɗanda ke da hannu a irin waɗannan laifuka tare da rushe cibiyoyin masu tada ƙayar baya.

Ta jaddada cewa rundunar sojin Nijeriya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta tabbatar da an hukunta masu aikata irin waɗannan laifuka tare da dawo da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.

A wata sanarwa ta daban, gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon Janar ɗin yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga, inda ta ce ya rasu ne sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita, da ta haɗa da ciwon sukari da hawan jini.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin tare da bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga jihar da Nijeriya baki ɗaya.

Ya kuma jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga da tabbatar da hukunta masu hannu a wannan aika-aika.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata