DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeWasanniBarcelona ta tsawaita kwantiragin Andreas Christensen zuwa 2028

Barcelona ta tsawaita kwantiragin Andreas Christensen zuwa 2028

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta sanar da tsawaita kwantiragin ɗan bayanta na ƙasar Denmark, Andreas Christensen, zuwa ranar 30 ga Yunin shekarar 2028.

Christensen mai shekaru 30, wanda tsohon kwantiraginsa ta ƙare a ƙarshen watan Yuni, ya amince da rage albashinsa domin ci gaba da zama a ƙungiyar, kamar yadda rahotanni daga Spain suka bayyana.

Barcelona ta tabbatar da yarjejeniyar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, tana mai cewa ɓangarorin biyu sun cimma matsaya kan sabon kwantiragin.

Christensen ya koma Barcelona daga Chelsea a shekarar 2022, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ƙungiyar lashe gasar La Liga a kakarsa ta farko.

Sai dai, ya sha fama da raunuka tun bayan zuwansa Camp Nou, lamarin da ya rage yawan wasannin da ya buga.

Tun da ya koma Barcelona, Christensen ya buga wasa 98, inda ya taimaka wa ƙungiyar lashe kofunan La Liga uku da kuma Copa del Rey, tare da wasu kofuna daban-daban.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata