DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiGwamna Uba Sani ya dauki nauyin iyalan malamar da aka kashe a...

Gwamna Uba Sani ya dauki nauyin iyalan malamar da aka kashe a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin iyalan marigayiya Ummulkhairi Usman Aliyu, malamar addinin Musulunci da wasu fusatattun matasa suka kashe tare da kona gawarta a Maraban Jos da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, marigayiyar ta rasa ranta ne bayan wasu mutane sun zarge ta da yunkurin satar yara a yankin Maraban Jos da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Gwamna Uba Sani ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayiyar a ranar Asabar, inda ya tabbatar musu cewa gwamnati za ta kula da mijinta da ‘ya’yanta hudu tare da daukar nauyin karatunsu.

Ya ce duk da cewa yana wata tafiya ta aiki a lokacin da abin ya faru, nan take ya umurci manyan jami’an gwamnati su kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamaciyar.

A cewar gwamnan, gwamnatin jihar na aiki tare da kwamishinan ‘yan sanda da jami’an DSS domin tabbatar da cewa an hukunta duk wadanda suka shiga cikin kisan.

Ya bayyana cewa mutane 41 tuni aka gurfanar da su kan laifin kisan kai, yayin da aka binciki wasu mutum 41, sannan aka gurfanar da wasu 30 kan zargin hada gangami ba bisa ka’ida ba.

Gwamna Uba Sani ya kuma bukaci a gudanar da cikakken bincike kan yadda jami’an tsaro suka gudanar da aikinsu a lokacin lamarin, musamman DPO na yankin Maraban Jos.

Ya ce gwamnati za ta tabbatar da kare rayukan jama’a tare da hana mutane daukar doka a hannunsu.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata