Gwamnatin jihar Osun ta sanar da cewa za ta garzaya babbar kotun tarayya domin ƙalubalantar matakin da hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin ƙasa tu’annati ta ɗauka na dakatar da amfani da asusun gwamnatin jihar.
Babban lauyan jihar kuma kwamishinan shari’a, Oluwole Jimi-Bada, ya ce Gwamna Ademola Adeleke ya ba shi umarnin shigar da ƙara bayan EFCC ta aika wa First Bank wasiƙar “Post No Debit”, wadda ke hana gudanar da mu’amala a asusun gwamnatin jihar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Jimi-Bada ya ce EFCC na da ikon binciken asusun gwamnati, amma ba ta da ikon dakatar da amfani da su ba tare da umarnin kotu ba.
“Na samu umarni daga gwamnan jihar na garzaya babbar kotun tarayya domin ƙalubalantar wannan mataki. EFCC na iya binciken asusun gwamnati, amma ba za ta iya dakatar da amfani da su ba tare da umarnin kotu ba,” in ji Jimi-Bada.
Ya ƙara da cewa matakin na iya kawo cikas ga gudanar da harkokin gwamnati, amma ya jaddada cewa za su tabbatar EFCC ta yi aiki cikin iyakokin doka.
Shi ma kwamishinan kuɗi na jihar, Sola Ogungbile, ya yi zargin cewa jami’an ‘yan sanda sun je babban reshen First Bank da ke Osogbo tare da kama wasu ma’aikatan bankin.
Ogungbile ya kuma musanta zargin cewa Gwamna Adeleke na amfani da kuɗaɗen gwamnatin jihar wajen yakin neman zaɓensa, yana mai kira ga EFCC da ta yi la’akari da tasirin da dakatar da asusun zai yi ga rayuwar al’ummar jihar.
Tun da farko, Gwamna Adeleke ya yi zargin cewa EFCC na shirin daskarar da dukkan asusun gwamnatin jihar da kuma na manyan jami’an gwamnati.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kai na jihar, Kolapo Alimi, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce idan har hakan gaskiya ne, to karan-tsaye ne ga doka kuma an yi hakan ne domin dakile ayyukan gwamnati gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
A cewar gwamnan, babu wata hujja ta doka da za ta bai wa EFCC damar daskarar da asusun gwamnatin jiha, yana mai cewa hukumar ba ta da wannan iko.
