Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce amfani da tsarin tsaron al’umma (community policing) na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro a faɗin Nijeriya.
Daily Trust ta ruwaito cewa Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne ranar Laraba a taron Arewa Awareness Summit on Unity Against Insecurity da aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. Chiroman Kano, Alhaji Adamu Lamido Sanusi, ne ya wakilce shi a taron.
Sarkin Musulmin ya ce ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa ba sai idan hukumomin tsaro sun yi aiki tare da al’ummomi. Ya bayyana cewa matasa da sauran mazauna yankuna sun fi kowa sanin abin da ke faruwa a muhallansu, don haka ya kamata a haɗa kai da su wajen tattara bayanan sirri da hana aikata laifuka.
“Ni da kaina na yi imani da tsarin tsaron al’umma. Idan ana son yaƙar laifi, dole ne a yi aiki tare da jama’a,” in ji Sarkin Musulmin.
Ya ƙara da cewa a kullum yana aiki tare da limamai, shugabannin addinai, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma domin ƙarfafa zaman lafiya da inganta tsaro.
Sarkin Musulmin ya bayyana tattara bayanan sirri a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen yaƙar laifuka, yana mai cewa mazauna yankuna sun fi baƙi sanin mutanen da ke aikata abubuwan da ba su dace ba.
“Mutanen da ke cikin al’umma, musamman matasa, sun fi kowa sanin yankunansu. Ta hanyar haɗin kai da hukumomin tsaro za a fi samun sahihan bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙar laifuka,” in ji shi.
Ya ce irin wannan haɗin gwiwa tsakanin al’umma da jami’an tsaro zai ƙara ƙarfi ga yaƙi da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.
Sarkin Musulmin ya kuma yabawa masu shirya taron, yana mai cewa lokaci ya yi da ya dace a ci gaba da musayar ra’ayoyi da ƙarfafa haɗin gwiwa domin nemo mafita ga matsalar tsaro, musamman a Arewacin Nijeriya.
Tun da farko, Babban Daraktan Arewa for Peace, Unity, Cohesion and Development Initiative (ACI), Dokta Abdullahi Idris, ya ce an shirya taron ne domin samar da hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya.
Shi ma Farfesa Mohammed Tasiu Dan Sabo, wanda ya wakilci Farfesa Ahmad Rufai, ya ce ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa ta hanyar amfani da ƙarfin soja kaɗai ba.
“Dole ne a haɗa tsaro da adalci da shugabanci nagari da kuma inganta rayuwar jama’a. Ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa ta hanyar aikin soja kaɗai ba,” in ji shi.
Taron na kwana guda ya haɗa sarakunan gargajiya, jami’an tsaro, shugabannin addinai, malamai, ƙungiyoyin fararen hula da ƙungiyoyin matasa domin tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya.
