DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasa'Bai kamata aikin EFCC na yaƙi da cin hanci ya zama makamin...

‘Bai kamata aikin EFCC na yaƙi da cin hanci ya zama makamin siyasa ba’

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan matakin da hukumar EFCC ta ɗauka na daskarar da asusun kuɗaɗen gwamnatin jihar Osun, yana mai cewa hakan na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar. Ya ce babu wani dalili da zai tabbatar da ɗaukar irin wannan mataki gabanin zaɓen gwamnan jihar Osun.

“Irin wannan mataki na iya kawo cikas ga gudanar da gwamnati, jinkirta biyan albashi, hana gudanar da muhimman ayyukan gwamnati da kuma haifar da yanayin tsoratarwa wanda bai dace da dimokuraɗiyya ba,” in ji Atiku.

Ya ce idan akwai zargin da ke buƙatar bincike, doka ta tanadi hanyoyin da ya kamata a bi, yana mai gargaɗin cewa bai kamata hukumomin yaƙi da cin hanci su yi abin da zai sa a ɗauka ana amfani da su wajen siyasa ba.

Atiku ya ce dimokuraɗiyyar Nijeriya ba ta dogara ga gudanar da zaɓe kaɗai ba, har ma tana buƙatar jama’a su amince cewa cibiyoyin gwamnati na aiki cikin adalci, ƙwarewa da ‘yancin kai.

“Yin amfani da hukumomin gwamnati ta hanyar da za ta nuna wariya ko son rai yana raunana amincewar jama’a da kuma tsarin dimokuraɗiyya. Hukumomin da aka kafa domin tabbatar da doka bai kamata su zama makamin siyasa ko tsoratar da abokan hamayya ba.”

Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yawan ɗaukar matakan da suka fi shafar jihohin da jam’iyyun adawa ke mulki.

A cewarsa, wannan mataki ya biyo bayan rikicin da ya shafi kuɗaɗen ƙananan hukumomin Osun, wanda ya ƙara ƙarfafa zargin cewa ana amfani da cibiyoyin gwamnati wajen takura wa ‘yan adawa.

Atiku ya buƙaci EFCC ta gaggauta janye matakin daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun.

“Daskarar da asusun gwamnatin jihar ba wai hari ne kan gwamnatin Osun kaɗai ba, hari ne kai tsaye kan al’ummar jihar, domin albashi, ayyukan gwamnati da rayuwar yau da kullum za su fuskanci matsala. Bai kamata a karkatar da aikin EFCC na yaƙi da cin hanci zuwa makamin siyasa kan gwamnatocin adawa ba.”

Ya kuma yi kira ga dukkan hukumomin da ke da ruwa da tsaki wajen gudanar da zaɓen gwamnan Osun da su kasance masu nuna adalci, kauce wa son rai da kuma bin tanadin kundin tsarin mulki.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata