DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaTinubu ya umarci EFCC ta buɗe asusun gwamnatin Osun

Tinubu ya umarci EFCC ta buɗe asusun gwamnatin Osun

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumar EFCC da ta garzaya kotu domin janye umarnin da ya bai wa hukumar damar daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun, yana mai cewa lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba, musamman ganin cewa saura kwanaki kaɗan a gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Laraba. A cikin sanarwar, Shugaba Tinubu ya ce ya samu labarin cewa EFCC ta samu umarnin kotu a ranar 5 ga Agusta, 2026, na daskarar da asusun gwamnatin Osun.

Shugaban ƙasar ya ce duk da cewa EFCC na da ikon gudanar da aikinta bisa doka, ya damu matuƙa da lokacin da aka ɗauki matakin, domin duk wani aiki da hukumomin gwamnatin tarayya suka yi, jama’a kan ɗora masa alhakin hakan.

“Na ji kunya ba saboda EFCC ta yi amfani da ikon da doka ta ba ta ba, amma saboda lokacin da ta ɗauki wannan mataki. Duk wani aiki da wata hukuma ta gwamnatin tarayya ta yi, jama’a kan danganta shi da ni a matsayin shugaban ƙasa, ko da ban san da shi ba.”

Tinubu ya ce tun bayan hawansa mulki ya kauce wa tsoma baki cikin ayyukan EFCC da sauran hukumomin bincike, domin ya yi imanin cewa dole ne su gudanar da aikinsu cikin ‘yanci, ƙwarewa da bin doka ba tare da tsoma bakin siyasa ba.

Sai dai ya ce duk da cewa bai samu cikakken bayani kan dalilan da suka sa EFCC ta nemi umarnin kotun ba, ya yi imanin cewa lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba.

“Jihar Osun na dab da gudanar da zaɓen gwamna. Saboda haka, bai kamata a yi wani abu da zai ba da tunanin cewa EFCC ko wata hukuma ta gwamnatin tarayya ana amfani da ita wajen yin tasiri kan zaɓen ba.”

Shugaban ƙasar ya ce saboda kare amincewar jama’a da sahihanci da adalcin tsarin dimokuraɗiyya, ya zama wajibi ya sa baki a lamarin.

“Saboda haka, na umarci EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin janye wannan umarni, tare da dakatar da duk wani matakin da ta fara ɗauka kan gwamnatin jihar Osun dangane da wannan batu.”

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata