Iran ta ce yiwuwar sake buɗe Mashigin Hormuz ga zirga-zirgar jiragen ruwa ya dogara ne da matakin da Amurka za ta ɗauka, tana mai zargin Washington da ci gaba da killace tashoshin ruwanta da kuma ɗaukar matakan da ke barazana ga tsaron yankin.
Gidan talabijin na Channels, ya ruwaito cewa kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya ce Iran ba ta tattauna wata yarjejeniya da Amurka ba, duk da ikirarin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi cewa Tehran na son cimma matsaya. Maimakon haka, ya ce Iran na aiki tare da ƙasar Oman domin tsara yadda za a gudanar da zirga-zirga a mashigin.
Iran da Oman sun amince kan hanyar da jiragen ruwa za su bi a mashigin Hormuz, kuma suna kammala shirye-shiryen tafiyar da mashigin tare. Sai dai Iran ta ce duk wata sauƙaƙawa za ta dogara ne da ko Amurka za ta kawo ƙarshen killace tashoshin ruwanta.
“An riga an amince kan tsarin hanyar da jiragen ruwa za su bi tsakanin ɓangarorin biyu. Idan wasu ɓangarori ba su kawo cikas ba, sanarwar haɗin gwiwa da ke ƙunshe da manyan yarjejeniyoyi na kan matakin ƙarshe na rubutawa,” in ji Baqaei.
Ya ƙara da cewa duk da ci gaban tattaunawa da Oman, hakan ba yana nufin mashigin a buɗe yake ga dukkan jiragen ruwa.
“Har yanzu abubuwan da ke haddasa rashin tsaro a Mashigin Hormuz suna nan daga ɓangaren Amurka, musamman killace tashoshin ruwan Iran da sauran matakan barazana ga muradun ƙasarmu.”
Rahoton ya ce Iran ta ci gaba da nuna iko a mashigin tun bayan yaƙin da ta ce Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a kanta a ranar 28 ga Fabrairu, inda ta yi barazanar ɗaukar mataki kan jiragen ruwan da ta ce ba su bi hanyoyin da ta amince da su ba.
A gefe guda kuma, hukumar tsaron harkokin ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce wani kyaftin ɗin jirgin dakon mai ya ba da rahoton jin ƙarar fashewa sau biyu yayin da yake ratsa mashigin, kilomita 17 kudu maso gabashin Kumzar na Oman, sai dai babu rauni ko lahani ga jirgin ba.
Haka kuma, mayaƙan Houthi na Yemen sun yi ikirarin cewa sun kai hari kan wasu jiragen dakon man fetur biyu na Saudiyya, yayin da hukumomin Saudiyya ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Rahoton ya kuma ce kafin rikicin ya ɓarke, kusan kashi ɗaya cikin biyar na man fetur da iskar LNG da ake fitarwa a duniya suna bi ta Mashigin Hormuz, lamarin da ya sa rikicin ke ci gaba da haifar da tashin farashin makamashi a kasuwannin duniya.
