Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama wani matashi ɗan shekara 27 mai suna Sada Tambai, bisa zargin kashe mahaifinsa mai shekara 80 a duniya, Adamu Tambai, a ƙaramar hukumar Bindawa.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 26 ga Satumba, 2026, kamar yadda DCL Hausa ta ruwaito.
Aliyu ya bayyana cewa a ranar 21 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 12:00 na rana, ofishin ’yan sanda na shiyyar Bindawa ya samu kiran gaggawa daga Hakimin Bindawa (Dan Yusufan Katsina), yana mai bayar da rahoton cewa an tsinci gawar Adamu Tambai, tsohon mai unguwar ƙauyen Mundadu mai shekara 80, a kwance a gaban gidansa ba tare da alamun numfashi ba.
Bayan samun rahoton, jami’an bincike sun garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka kwashe dattijon zuwa asibiti mafi kusa domin ba shi kulawar gaggawa, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
Binciken farko da ’yan sanda suka gudanar ya kai ga cafke ɗan mamacin, Sada Tambai. A yayin da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya buga wa mahaifin nasa sanda a kai, lamarin da ya yi sanadin munanan raunukan da suka yi ajalinsa.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya ba da umarnin mayar da binciken zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike mai zurfi, inda ya jaddada cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zaran an kammala bincike.
