Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa a wani lokaci ‘yan Najeriya sun shirya biyan har Naira 10,000 kan kowace lita ta man fetur amma duk da haka ba a samun sa a kasuwa.
Akpabio ya bukaci al’umma su ci gaba da hakuri da gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa gyare-gyaren tattalin arzikin da ake yi na fara haifar da sakamako mai kyau, musamman a bangaren man fetur.
