Ana ci gaba da samun kiraye-kiraye ga tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, da ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, yayin da ake fuskantar sauye-sauye dalilin zuwan haɗakar siyasa a cikin jam’iyyun adawar ƙasar.
Jonathan ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa ga marigayi Umaru Musa Yar’Adua daga shekarar 2007, har zuwa rasuwarsa a watan Mayun 2010, inda daga nan aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.
Daga bisani, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2011, amma ya sha kaye a yunƙurinsa na zarcewa a 2015 bayan ya fuskanci tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
