DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, April 15, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta cire zargin daukar nauyin ta'addanci cikin jerin zarge-zargen da...

Gwamnatin Nijeriya ta cire zargin daukar nauyin ta’addanci cikin jerin zarge-zargen da take yi wa Abubakar Malami

Gwamnatin Nijeriya ta gyara tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da ɗansa Abdulaziz Malami, inda ta cire zargin daukar nauyin ta’addanci, tare da mayar da hankali kan mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Gidan talabijin na Arise ya rawaito Lamarin ya faru ne a kotu a ranar Larabar nan, inda lauyan hukumar tsaron farin kaya ta DSS, Akinlolu Kehinde, ya sanar da kotu cewa an gyara tuhumar tare da neman a maye gurbin tsohuwar takardar kara da sabuwar wadda tuhumar ta shafi zargin mallakar bindigogi ba tare da izini ba.

Lauyan wadanda ake kara, Shaibu Aruwa, ya tabbatar da cewa an bai wa abokan aikinsa sabuwar tuhumar, kuma ba su da wata adawa da a karanta ta a gaban kotu.

Bayan karanta tuhumar a kotun, Malami da ɗansa sun musanta zargin, daga nan kotu ta dage shari’ar domin ci gaba da sauraron karar a gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata