DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Ogun ta bai wa ma'aikata alawus tare da rage kwanakin aiki

Gwamnatin Ogun ta bai wa ma’aikata alawus tare da rage kwanakin aiki

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya amince da ba ma’aikatan gwamnati hutu na rana guda a kowane mako tare da ba su alawus na sufuri na naira 10,000 domin rage radadin halin da ake ciki na tsadar rayuwa.

Wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar ya fitar, ta bayyana cewa wannan mataki wani bangare ne na tallafin gaggawa da gwamnatin ta bullo da shi domin rage wa ma’aikata radadin tsadar sufuri, musamman bayan karin farashin man fetur da ya jawo hauhawar kudin zirga-zirga.

Shirin zai fara aiki daga watan Afrilu na shekarar 2026, kuma ana sa ran zai gudana na tsawon watanni uku a matakin farko, inda gwamnati za ta duba tasirinsa kafin yanke hukuncin ci gaba da shi ko akasin haka.

A karkashin tsarin, ma’aikatan da suka cancanta za su rika samun rana guda na hutu a kowane mako, wanda hakan zai rage yawan kwanakin da suke zuwa aiki daga biyar zuwa hudu a mako.

Sai dai gwamnati ta bayyana cewa akwai wasu rukunin ma’aikata da ba za su amfana da hutun mako-mako ba saboda muhimmancin aikinsu, ciki har da ma’aikatan lafiya, malamai, jami’an tsaro da wasu manyan jami’an gwamnati.

Duk da haka, an tabbatar da cewa ko wadannan rukunin ma’aikata da aka ware daga hutun za su ci gaba da karbar alawus na sufuri na naira 10,000 kamar sauran ma’aikata, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya wallafa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata