DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 17, 2026
HomeLabaraiCike nake da aniyar gina kasa mai zaman lafiya – Shugaban Nijeriya...

Cike nake da aniyar gina kasa mai zaman lafiya – Shugaban Nijeriya Bola Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyarsa ta gina ƙasa mai zaman lafiya da wadata ta hanyar ci gaba da gyaran tattalin arziki da zai bai wa kowa damar cin gajiyar ci gaba.

Shugaba Tinubu a yayin jawabinsa as lokacin da ya karɓi tawagar Renewed Hope Ambassadors ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da dama ga talakawa da matasa, tare da tabbatar da bin doka, raba madafun iko, da kuma kare haƙƙin jama’a.

Shugaban kasar ya ma yi kira ga ‘yan Nijeriya su guji yaɗa labaran ƙarya tare da ba da goyon baya ga sauye-sauyen da ake yi domin bunƙasa tattalin arziki da haɗin kan ƙasa, yayin da manyan jiga-jigan APC da gwamnoni da dama suka halarci taron tare da bayyana goyon bayansu ga manufofin gwamnatin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata