Gwamnan Plateau Caleb Mutfwang ya gana da tsofaffin gwamnonin jihar domin tattauna matsalar tsaro da ke kara ta’azzara a wasu sassan jihar.
Taron ya gudana ne a gidan gwamnati da ke Jos, inda aka mayar da hankali kan hare-haren da ake kaiwa al’ummomin karkara a ‘yan kwanakin nan, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsofaffin gwamnonin jihar kamar Fidelis Tapgun, Joshua Dariye, Jonah Jang da kuma Simon Lalong, inda suka tattauna hanyoyin dawo da zaman lafiya.
A nasa bangaren, gwamna Mutfwang ya ce taron ya mayar da hankali kan walwala da ci gaban al’ummar jihar, tare da nazarin hare-haren da suka faru kwanan nan a yankunan karkara.
Ya kara da cewa shugabannin sun tattauna kan hanyoyin inganta zaman lafiya mai dorewa, karfafa hadin kai da kuma tabbatar da zaman tare tsakanin al’ummar jihar ba tare da wariya ba.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar hare-hare a jihar Filato, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi, tare da kara jefa fargaba a zukatan mazauna yankin.
