Rahotanni sun bayyana cewa ɗan wasan baya na kasar Austria, David Alaba, na dab da raba gari da ƙungiyar Real Madrid a ƙarshen wannan kakar.
An ruwaito cewa kwantiragin Alaba na shirin ƙarewa, kuma ƙungiyar ba ta nuna alamun sabunta masa kwangila ba, lamarin da ke sa yiwuwar ya fita a matsayin ‘free agent’ a lokacin bazara.
Majiyoyi sun ce tuni wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Turai da wajen nahiyar suka fara nuna sha’awa wajen ɗaukar sa, duk da cewa har yanzu ba a fara tattaunawa a hukumance ba.
Alaba, wanda ya shahara a matsayin ɗan wasan baya mai kwarewa, ya taka muhimmiyar rawa a nasarorin Real Madrid tun zuwansa kulob ɗin.
