DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 17, 2026
HomeWasanniAshley Cole ya zama mai horar da 'yan wasa a kasar Italiya

Ashley Cole ya zama mai horar da ‘yan wasa a kasar Italiya

Tsohon dan wasan baya na Ingila Ashley Cole ya fara sabon babi a rayuwarsa ta kwallon kafa bayan shiga harkar horarwa a matakin babban koci a kasar Italiya.

Rahotanni sun nuna cewa Cole ya zama sabon babban koci na kungiyar Cesena FC, wanda wannan shi ne karon farko da yake rike da mukamin horar da babbar kungiya a rayuwarsa.

Tsohon dan wasan na Ingila, wanda ya buga wa kasarsa wasanni sama da 100, ya bayyana cewa rashin samun dama a Ingila ne ya sa ya yanke shawarar komawa kasashen waje domin neman ci gaba a harkar horarwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Cole ya ce ya dade yana kokarin samun damar zama babban koci a Ingila, amma sau da dama ana kin ba shi damar ne da hujjar cewa bai da gogewar da ake bukata.

Ya kara da cewa wannan hali ya sa ya fara jin takaici, domin a cewarsa, babu yadda za a samu gogewa idan ba a ba mutum dama ba.

Kafin wannan matsayi, Cole ya rike mukamai daban-daban na mataimakin koci a kungiyoyi da dama da suka hada da Chelsea da Everton, sannan ya yi aiki da tawagar matasan Ingila.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata