An samu cikas a shirin da ake yi na sauya sheƙar Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed zuwa APC bayan rashin jituwa kan tsarin rabon iko a jihar.
Shugaban ɓangaren PDP na Tamnmu Turaki a Bauchi Sama’ila Burga shi ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabardinnan.
Ya ce tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnan, ɓangarensa da shugabannin APC ta tsaya cik ne bayan jam’iyyar APC ta ƙi amincewa da tsarin rabon iko na kashi 60 zuwa 40.
Burga ya ce tattaunawar ta fara ne ta hannun APC ta hanyar gwamnan, tare da shugabannin ƙasa na jam’iyyar da kuma Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, wanda ya kai ziyara Bauchi domin lallashin Bala Mohammed ya shiga APC.
Ya kuma ce tsarin da suka gabatar shi ne irin wanda aka yi amfani da shi a wasu jihohin da gwamnoni suka koma APC.
Ya ƙara da cewa bayan tuntuba da masu ruwa da tsaki, sun yanke shawarar dakatar da tattaunawar gaba ɗaya, tare da bayyana cewa yanzu suna duba wasu jam’iyyu daban domin gano mafita mafi dacewa da muradun al’ummar Bauchi.
Lamarin ya nuna cewa shirin komawar gwamnan APC ya tsaya cik a halin yanzu.
