DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, May 17, 2026
HomeLabaraiJAMB ta kama mahaifi da dalibai biyu bisa zargin samar da sakamako...

JAMB ta kama mahaifi da dalibai biyu bisa zargin samar da sakamako na bogi

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya JAMB ta sanar da cafke ɗalibai biyu da wani mahaifi guda saboda zargin ƙirƙirar sakamakon jarabawar shiga jami’a ta shekarar 2026 wato UTME ta hanyar amfani da fasahar basirar na’urar AI.

A cikin sanarwar da kakakin hukumar JAMB Fabian Benjamin ya fitar ranar Juma’a, hukumar ta ce an kama mutanen ne bayan sun yi amfani da hanyoyin sauya saƙonnin sakamakon jarabawa da hukumar ke aikawa ta SMS domin ƙara ko rage maki da nufin yaudarar iyaye.

Sanarwar ta ce hakan ya faru ne bayan fitar da sakamakon ɗalibai 632,788 da suka rubuta jarabawar ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilu.

JAMB ta gargadi ɗalibai kada su yi yunkurin sauya sakamako da ake aikawa ta lambobin hukuma na 55019 da 66019.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ba’a fara buga takardar sakamako ta hukuma ba tukuna, kuma za a sanar idan an buɗe.

Jarabawar ta UTME ta 2026 an fara ta ne ranar 16 ga Afrilu kuma za ta gudana har zuwa 22 ga watan a cibiyoyi daban-daban na ƙasar nan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata