Wasu ’yan Najeriya biyu Akinade Raheem da Abayomi Eletu na fuskantar hukuncin daurin shekaru 50 a gidan yari kowannensu bayan an zarge su da shirya wata badakala ta damfarar haraji da ta kai sama da dala miliyan 100 daga Hukumar Tara Haraji ta Amurka.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta fitar ranar Laraba, an ce mutanen biyu sun hada baki da wasu abokan aikinsu wajen amfani da bayanan wasu mutane da aka sace, suna kwaikwayon masu lissafin haraji da masu biyan haraji domin neman kudaden fansho na bogi daga hukumar harajin ta Amurka IRS.
Rahoton ya ce daga shekarar 2018 zuwa 2023, Raheem mai shekaru 43 da Eletu mai shekaru 42, mazauna Amurka da Birtaniya, sun samu bayanan sirri da suka hada da suna, adireshi da lambobin tsaro na jama’a, sannan suka yi amfani da su wajen bude asusun intanet a IRS da neman bayanan masu biyan haraji.
Ana zarginsu da gabatar da sama da takardun haraji 300 na bogi domin neman dawo da sama da dala miliyan 100.
Rahotanni sun ce Eletu na fuskantar karin tuhume-tuhume da suka hada da damfarar wasiku, damfarar sadarwa, amfani da bayanan katin kudi ba bisa ka’ida ba da kuma satar bayanan sirri, yayin da Raheem ke fuskantar tuhume-tuhume makamantan haka.shugabasshugaba
Hukumomi sun ce Eletu an kama shi a Birtaniya bisa bukatar Amurka, yayin da ake zargin sun rika canza adireshin masu biyan haraji, sayen motocin da aka yi amfani da su da wasu kayayyaki tare da tura wasu zuwa Najeriya.
