Sadakin tsabar zinariya guda 12 da kimarsa ta kai kusan Naira miliyan 9.6 ne ya fito fili a ɗaurin auren Aisha, ‘yar Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da Muhammad, ɗan Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe.
Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da ɗaurin auren ne a Masallacin Shehun Borno da ke Maiduguri, inda Babban Limami, Sheikh Imam Shettima Mamman Saleh, ya jagoranci ɗaurin tare da yi wa ma’auratan addu’ar samun albarka.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa manyan ‘yan siyasa da attajirai daga ciki da wajen Nijeriya sun halarci bikin, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, attajirin Afirka Aliko Dangote, Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin.
Haka kuma gwamnonin jihohi da dama sun halarci bikin, ciki har da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, Gwamnan Kaduna, Uba Sani, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda, Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu, da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.
A wajen bikin, Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ne ya wakilci angon yayin ɗaurin auren, yayin da hamshaƙin ɗan kasuwa kuma wanda ya kafa kamfanin Oriental Energy, Muhammadu Indimi, ya wakilci amaryar.
