DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 18, 2026
HomeLabaraiTsohon shugaban hukumar NFF Ibrahim Galadima ya Rasu

Tsohon shugaban hukumar NFF Ibrahim Galadima ya Rasu

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFA wacce yanzu ake kira Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF Alhaji Ibrahim Galadima, ya rasu yana da shekara 78.

Ibrahim Galadima wanda ya kafa ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars FC ya rasu bayan fama da doguwar jinya.

A cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na Kano Pillars ya fitar ranar Asabar, kulob ɗin ya tabbatar da rasuwar marigayin.

An haifi marigayi Galadima ranar 15 ga Fabrairun shekarar 1948, kuma an bayyana shi a matsayin fitaccen jami’in kula da harkokin ƙwallon ƙafa, sa’annan ɗaya daga cikin manyan mutane masu tasiri a harkokin wasanni a Najeriya.

Ya jagoranci NFA daga shekarar 2002 zuwa 2006, inda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa ƙwallon ƙafar Najeriya da kuma wakilcin ƙasar a duniya kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sanarwar ta ce marigayin ya kuma riƙe muƙamin Shugaban Hukumar Wasanni ta jihar Kano, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka harkokin wasanni tun daga matakin matasa har zuwa manyan ‘yan wasa.

Haka kuma, yana cikin waɗanda suka kafa Kano Pillars FC, inda ya aza harsashin nasarorin da kulob ɗin ke morewa a yau.

Sanarwar ta ce za a yi sallar jana’izarsa ranar Lahadi da ƙarfe 10:00 na safe a masallacin Waje da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano.

Shugaban Kano Pillars da babban manajansa sun miƙa ta’aziyya ga iyalansa, gwamnatin Kano da al’ummar jihar, da ma daukacin al’ummar ƙwallon ƙafar Najeriya, tare da addu’ar Allah ya jikansa da Aljannatul Firdausi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata