DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 19, 2026
HomeLabarai'Najeriya za ta tura sojoji a 200 Türkiye domin horaswa'

‘Najeriya za ta tura sojoji a 200 Türkiye domin horaswa’

Gwamnatin Nijeriya ta amince da tura jami’an runduna ta musamman 200 zuwa ƙasar Türkiye domin samun horo na soja, a wani sabon shiri na ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

Ministan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ne ya bayyana hakan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito, yayin da yake halartar taron diflomasiyya na Antalya Diplomacy Forum (ADF2026) a Antalya, Türkiye.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ministan ya yi bayanin ne bayan ganawa da takwaransa na Türkiye, Yasar Guler, inda suka tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da kuma horar da sojoji.

A cewarsa, gwamnatin Türkiye ta ware guraben horo ga jami’an rundunar musamman 200 daga Nijeriya, kuma za a tura su da zarar ya koma gida daga taron.

Ministan ya ce wannan horo wani ɓangare ne na yarjejeniyar horarwa da atisayen soji da ƙasashen biyu za su rika yi tare, inda ya ƙara da cewa ana sa ran za a gudanar da atisayen farko daga baya a cikin shekarar nan.

Haka kuma, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa Nijeriya da Türkiye sun cimma matsaya kan haɗin gwiwa wajen kera kayan aikin soja da kuma musayar fasahar tsaro.

Ya ce Türkiye ta samu gagarumar nasara wajen samar da kayan aikin soja a cikin gida, abin da Nijeriya ke son koya domin bunƙasa masana’antar tsaro a ƙasar.

Ministan ya kuma tuna cewa ƙasashen biyu sun daɗe suna hulɗa tun bayan samun ‘yancin kan Nijeriya a shekarar 1960, yana mai cewa Türkiye na ɗaya daga cikin ƙasashen da Nijeriya ke kallon su a matsayin abokai na kusa.

A cewarsa, yayin da Nijeriya ta kwashe kusan shekaru 17 tana yaƙi da ‘yan ta’adda da sauran hare-haren ta’addanci, Türkiye kuma ta shafe kusan shekaru 40 tana fama da irin wannan barazana, don haka ƙasashen biyu na da abubuwa da dama da za su koya daga juna.

Taron Antalya Diplomacy Forum na bana ya samu halartar mahalarta daga kusan ƙasashe 150, ciki har da shugabannin ƙasashe, ministoci, jami’an diflomasiyya da masana daga sassa daban-daban na duniya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata