DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 19, 2026
HomeLabaraiNijeriya da Türkiye za su gina cibiyar horas da sojoji a Nijeriya

Nijeriya da Türkiye za su gina cibiyar horas da sojoji a Nijeriya

Nijeriya da ƙasar Türkiye sun cimma yarjejeniya kan gina babbar cibiyar horas da sojoji a Nijeriya domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar da kuma inganta horar da jami’an rundunar soji.

Kamar yadda sanarwar Ma’aikatar Tsaro ta Nijeriya ta bayyana, Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya tattauna da takwaransa na Türkiye, Yasar Guler, a yayin taron Antalya Diplomacy Forum na shekarar 2026.

Jami’ar hulɗa da yaɗa bayanai ta ma’aikatar tsaron Nijeriya, Queeneth Iheoma-Hart, ta ce za a kafa cibiyar horaswar a wani wuri da ke bakin teku a Nijeriya, yayin da za a fara aiki da wani wuri na wucin gadi kafin kammala ginin cibiyar.

Ta ce shirin zai ba jami’an rundunar sojin Nijeriya damar samun horo a fannoni da suka haɗa da ayyukan rundunar musamman, yaƙi da ta’addanci, haɗa bayanan leƙen asiri, yaƙi da jiragen sama marasa matuki, da kuma shirin tura sojojin zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa haɗin gwiwar zai haɗa da musayar fasahar soja, haɗin gwiwa wajen kera kayan aikin tsaro, da kuma inganta tsarin sa ido ta hanyar amfani da na’urorin zamani kamar jiragen sama marasa matuki da tauraron ɗan adam.

Bugu da ƙari, yarjejeniyar ta shafi inganta tsaron iyakoki, musayar bayanan sirri tsakanin ƙasashen biyu, da kuma shirin taimakawa wajen dawo da tsofaffin mayaƙa cikin al’umma bayan sun ajiye makamai.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa wannan yarjejeniya babban ci gaba ne a dangantakar tsaro tsakanin Nijeriya da Türkiye, yana mai cewa gwamnati na da niyyar ganin an aiwatar da matakan da aka amince da su domin ƙarfafa tsaron ƙasar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata