Farashin doya ya ci gaba da hauhawa a kasuwannin Lagos, inda masu saye da sayarwa ke kokawa kan tsadar kayayyakin abinci saboda karin kudin sufuri da karancin kayan gona a kasuwa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa ‘yan kasuwa da masu amfani da kayayyaki sun bayyana yadda kudin mota da wahalar kai kaya ke tasiri wajen sayen doya Legas.
A manyan kasuwanni irin su Oyingbo Market da Mile 12 Market ana samun farashi mai sauki fiye da kananan kasuwanni, amma kudin mota na hana wasu anfani da hakan.
Malam Ibrahim Hassan ya ce sabbin gonakin doya ba su gama fitowa ba tukuna, shi ya sa tubar doya da ake sayarwa tsakanin naira 2,500 zuwa 3,000 yanzu ka iya ninkuwa daga nan zuwa watan Agusta.
Haka kuma Hajiya Jumoke Fakunle ta ce girman doya ne ke kayyade farashinta, yayin da wasu ke cewa doyar da aka sayar tsakanin naira 1,200 zuwa 2,000 a shekarar 2025 yanzu ta koma tsakanin naira 2,500 zuwa 3,500.
Masu saye kuwa sun ce suna duba nisan kasuwa da kudin mota kafin su yanke shawarar inda za su saya.
Wasu sun ce suna samun sauki a manyan kasuwanni, yayin da wasu ke ganin sayen kusa da gida ya fi musu amfani saboda rage kashe kudin sufuri.
