DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, May 14, 2026
HomeLabaraiNi ɗan siyasa ne mai zaman kansa yanzu — Gwamna Bala Mohammed

Ni ɗan siyasa ne mai zaman kansa yanzu — Gwamna Bala Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana kansa a matsayin “ɗan siyasa mai zaman kansa,” yana mai cewa a halin yanzu ba shi da cikakkiyar alaƙa da kowace jam’iyya.

BalbGwamnan ya faɗi hakan ne ranar Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin jigon jam’iyyar ADC, Peter Obi, tare da wasu masu ruwa da tsaki daga yankin Kudu maso Gabas a Bauchi.

Bala Mohammed ya ce ganawar ta mayar da hankali ne kan haɗin kan ƙasa da haɗin gwiwa, ba tare da la’akari da jam’iyya ba, yana mai cewa “dukkanmu muna cikin ɓangaren adawa.”

Ya ƙara da cewa tattaunawar na cikin shirin daidaita sabbin tsare-tsaren siyasa gabanin zaɓuka masu zuwa, yana mai cewa dole ne a ƙarshe su sami wata kafa ta siyasa domin cimma manufofinsu.

Shi ma Peter Obi ya ce ziyarar ta sa ne domin ƙarfafa haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin yankuna, yana mai cewa ba batun sauya jam’iyya ba ne, sai dai gina ƙasa mai kyau.

Ganawar ta samu halartar wasu jiga-jigan Kudu maso Gabas ciki har da tsohon gwamnan Imo, Achike Udenwa, da sanatoci Enyinnaya Abaribe da Victor Umeh.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata