Madugun adawa a Nijeriya Atiku Abubakar, ya gargadi masu tunanin dakatar da yakin neman zabe a wasu sassan arewacin ƙasar.
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriyan Atiku ya ce hakan zai tauye hakkin kundin tsarin mulki tare da kara fargabar hana jama’a damar kada kuri’a.
A wata sanarwa a mai taimaka masa na musamman kan julda da jama’a Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce matsalar tsaro babbar barazana ce ga kasa, amma bai kamata a yi amfani da ita wajen hana jama’a shiga harkokin dimokuradiyya ba.
Ya ce hakkin kada kuri’a da shiga zabe hakki ne na asali da ba za a tauye ba ta kowace hanya.
Ya kara ewa duk wani yunkuri na dakatar da harkokin siyasa a jihohin Arewa zai haifar da zargin wariya da hana wakilci ga al’umma.
Atiku ya bukaci hukumar zabe ta Nijeriya INEC, hukumomin tsaro da gwamnatin Shugaba Tinubu su fito su fayyace matsayinsu, tare da tabbatar wa ’yan Najeriya cewa babu wani bangare na kasar da za a hana hakkinsa na kundin tsarin mulki.
Wannan na zuwa ne bayan Sanata Abdul Ningi ya bukaci Majalisar dattawa ta yi la’akari da dakatar da harkokin siyasa a jihohin da ke fama da hare-haren ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
