Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya sake jaddada cewa matatun man fetur na Nijeriya da ke Port Harcourt, Warri da Kaduna ba za su taba yin aiki yadda ake so ba, duk da kokarin neman sababbin abokan hulɗa da ake yi domin tafiyar da su.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Sony Irabor Live ya watsa a daren Asabar, inda ya ce tun yana mulki ya gargadi jama’a cewa matatun ba za su yi nasara ba.
Ya ce ya taba neman kamfanin Shell ya karɓi kaso 10 cikin 100 tare da kula da matatun, amma kamfanin ya ƙi.
Tsohon shugaban ya ce jami’an Shell sun shaida masa cewa ribarsu mafi yawa tana bangaren hako mai, ba tace mai ba.
Haka kuma sun ce matatun Nijeriya ƙanana ne idan aka kwatanta da na duniya, ba a kula da su yadda ya dace, sannan akwai cin hanci da rashawa a cikinsu.
Obasanjo ya ce daga baya attajiri Aliko Dangote ya bayar da dala miliyan 750 domin mallakar kaso 51 cikin 100 na matatu biyu, kuma an biya kuɗin.
Sai dai yayi zargin cewa bayan ya bar mulki, marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya soke yarjejeniyar bayan matsin lamba daga NNPC.
Obasanjo ya ƙara da cewa an kashe kusan dala biliyan 16 wajen gyaran matatun, duk da cewa har yanzu ba su kai matsayin da za su iya gogayya da sabuwar matatar Dangote Refinery ba.
Ya ce shugaban NNPC na yanzu, Bayo Ojulari, shi ne kaɗai ya faɗi gaskiyar halin da suke ciki.
