ShugabanNijeriya Bola Ahmed Tinubu ya daga likkafar Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin Ministar Harkokin Ƙasashen Waje, inda ta bar mukamin karamar minista da take riƙe da shi a ma’aikatar.
Wannan daga daraja ya biyo bayan murabus ɗin Yusuf Tuggar domin tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi a zaɓen 2027.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya hannu a ranar Laraba.
Onanuga ya kuma sanar da naɗin Sola Enikanolaiye daga jihar Kogi a matsayin karamin ministan harkokin ƙasashen waje, sai dai yana jiran amincewar majalisar dattawa.
Kafin wannan naɗi, Enikanolaiye ya kasance babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin ƙasashen waje da hulɗar ƙasa da ƙasa.
Bianca Odumegwu-Ojukwu, matar marigayi Emeka Odumegwu-Ojukwu, ta taba zama jakadiyar Nijeriya a Spain da kuma daga baya a Italiya, kafin a naɗa ta karamar ministar harkokin ƙasashen waje a 2023 karkashin gwamnatin Tinubu.
Shi kuma Tuggar, wanda ya fara aiki a matsayin ministan harkokin ƙasashen waje tun watan Agustan 2023, ya yi murabus domin fafutukar neman kujerar gwamnan Bauchi a zaɓen 2027.
A watan Maris da ya gabata, fadar shugaban ƙasa ta fitar da wata sanarwa ta hannun sakataren gwamnatin tarayya wadda ta umarci duk ministocin da ke da burin siyasa su yi murabus kafin ranar 31 ga Maris.
Enikanolaiye na da gogewar aikin diflomasiyya sama da shekaru 30, inda ya taba zama sakatare na dindindin a ma’aikatar harkokin ƙasashen waje, tare da rike mukamai a Addis Ababa, Belgrade, Ottawa, London da New Delhi.
Shugaba Tinubu ya ce waɗannan naɗe-naɗen na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na sake fasalin manufofin harkokin ƙasashen waje na Nijeriya domin inganta aiki, ƙarfafa hulɗa ta dabaru da kuma bunƙasa dangantaka da ƙasashen duniya.
Ya kuma bukaci sabbin ministocin da su mayar da hankali wajen kare muradun Nijeriya, inganta diplomasiyyar tattalin arziki, tabbatar da zaman lafiya a yankuna, da kuma kare jin daɗin ‘yan ƙasar a gida da waje.
