Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ayyana Juma’a, 1 ga watan Mayu 2026, a matsayin ranar hutun domin bikin ranar ma’aikata ta bana.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnati, inda ya taya ma’aikatan Nijeriya murna kan wannan rana.
A cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta sanya hannu a ranar Alhamis, ministan ya yaba wa ma’aikata a fadin ƙasar kan jajircewarsu da gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban ƙasa.
Ya jaddada cewa ƙoƙarin ma’aikatan Nijeriya na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki da ci gaban ƙasa, tare da kira gare su da su ci gaba da nuna kishin ƙasa, ƙwazo, da kuma sadaukar da kai a aikinsu.
Ministan ya kuma tabbatar da kudurin gwamnatin tarayya na inganta jin daɗin ma’aikata da tsaronsu, tare da samar da yanayi mai kyau da zai ƙarfafa bunƙasar tattalin arziki.
Yayin da yake yi wa ma’aikata fatar gudanar da bikin lafiya da nasara, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su zauna lafiya, su bi doka, tare da amfani da wannan rana wajen tunani kan muhimmancin haɗin kai da ƙwazo wajen gina ƙasa.
