DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, September 26, 2026
HomeSiyasaMinistan shari'ar Nijeriya na goyon bayan soke rajistar jam'iyyun da ba su...

Ministan shari’ar Nijeriya na goyon bayan soke rajistar jam’iyyun da ba su cika sharudda ba, ciki hada ADC

Babban Lauyan Nijeriya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, ya nuna goyon baya ga wata kara da ke neman a soke rijistar wasu jam’iyyun siyasa, ciki har da ADC, bisa zargin karya tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

Wannan matsaya ta ministan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka gabatar a gaban babbar kotu da ke Abuja, a karar mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026, kamar yadda takardu daga Tribune Online suka nuna. A karar, an hada da Hukumar zaben INEC, AGF, ADC, Action Alliance, Action Peoples Party, Accord da Zenith Labour Party a matsayin wadanda ake kara.

Ministan, wanda aka sanya a matsayin wanda ake kara na biyu, ya ce ya amince da karar “gwargwadon nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa,” yana mai jaddada cewa shi ne mai kula da kare kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Ya ce kundin tsarin mulki ya ba shi damar shigar da kara, karewa ko marawa duk wani mataki baya domin tabbatar da bin doka. Haka kuma ya bayyana cewa bisa sashe na 150(1) na kundin tsarin mulki, yana da alhakin aiwatar da dokoki ciki har da dokar zabe.

Lateef ya kara da cewa ofishinsa na da rawa biyu da zai iya takawa—wakiltar gwamnati da kuma kare hakkin ‘yan kasa—don haka dole ne ya yi aiki domin amfanin jama’a, tare da tabbatar da cewa ana fassara da aiwatar da dokoki yadda ya kamata.

A cewarsa, goyon bayan karar na cikin aikinsa na kare kundin tsarin mulki da kuma taimakawa wajen samun adalci, musamman ga ‘yan kasa da ba su da damar kalubalantar karya doka.

Ya kuma ce ci gaba da barin jam’iyyun da ba sa cika sharudda zai kara tsawaita takardun zabe, ya nauyaya kudin gwamnati, kuma ya dagula tsarin gudanar da zabe.

AGF ya jaddada cewa hukumar zaben INEC ba ta da damar barin jam’iyyun da suka gaza cika sharuddan sashe na 225A na kundin tsarin mulki su ci gaba da zama a rijista.

Ya kara da cewa duk wata gazawa ko kin daukar mataki daga INEC wajen soke irin wadannan jam’iyyu na nufin ci gaba da karya doka, wanda za a iya kalubalanta a kotu.

Wannan shari’a na daga cikin sabuwar takaddamar shari’a da ke kunno kai kan matsayin jam’iyyun siyasa da kuma ikon INEC karkashin kundin tsarin mulki da dokar zabe a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata