Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya bayyana goyon bayansa ga Alhaji Baba Malam Wali a matsayin wanda yake so ya gaje shi a kujerar gwamna.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Yobe, wanda aka gudanar a Abuja a daren Laraba. Taron ya bayyana Wali a matsayin gogaggen masani mai kwarewa da ya dace da jagoranci da gudanar da mulki.
Masu ruwa da tsakin sun ce Wali ya dade yana taka rawa a gwamnatoci daban-daban a jihar, wanda hakan ke kara masa karfi wajen ci gaba da manufofin bunkasa jihar. Jam’iyyar ta kuma yanke shawarar amfani da tsarin sulhu (consensus) wajen zabar ‘yan takararta, tare da mara wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Gwamna Buni da shugaban dandalin masu ruwa da tsaki na jihar, Sanata Ibrahim Geidam, sun jaddada cewa jam’iyyar za ta ci gaba da tattaunawa domin karfafa hadin kai.
Wali ya fito ne daga karamar hukumar Nguru a yankin Yobe ta Arewa, yankin da bai taba samar da gwamna ko mataimakin gwamna ba tun 1999—abin da ke kara masa karfi.
Wali ya yi digirinsa na farko da na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, sannan ya fara aiki a Hukumar Raya Yankin Tafkin Chadi (CBDA), kafin ya koma MAMSER a matsayin jami’in wayar da kan jama’a.
Daga bisani ya yi aiki a ofishin gwamnan jihar Borno a matsayin babban jami’in bincike, sannan ya zama shugaban ma’aikata (Chief of Staff) ga gwamnan soja na jihar. Bayan ya zama babban sakatare, ya yi aiki a ma’aikatun wasanni, sufuri, makamashi, muhalli da kuma harkokin gudanarwa.
An kuma zabe shi ya halarci shirin horo na manyan jami’ai a National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS), inda ya samu lambar mni.
Bayan dawowarsa daga NIPSS, ya sake aiki a ofishin gwamna kafin daga bisani a nada shi sakataren gwamnatin jihar Yobe, mukamin da ya rike a karkashin Geidam da Buni. A watan Maris, ya kafa tarihi a matsayin wanda ya fi kowa dadewa yana rike mukamin SSG a Nijeriya, kamar yadda kungiyar gwamnonin APC ta tabbatar.
A wani bangare kuma, Gwamna Buni ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar sanatan Yobe ta Gabas a zaben gaba, bayan ya karbi fom din takara sakamakon matsin lamba daga magoya baya.
Ya ce zai ci gaba da yi wa al’ummar jihar hidima da kwarewa. Kujerar sanatan na hannun Sanata Musa Mustapha (Kulas), surukin Geidam, wanda kafin haka ake ganin zai iya zama daya daga cikin ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar APC.
