Madugun adawa a Nijeriya Atiku Abubakar, ya tabbatar da shirinsa na kai ziyara zuwa ƙasar Amurka domin jawo hankalin ƙasashen duniya kan tabarbarewar tsaro, ta’azzarar matsin tattalin arziki da kuma raguwar ingancin shugabanci a kasar.
A yayin wannan ziyara da yake shirin yi, Atiku zai gana da masu ruwa da tsaki a bangarori da dama a Amurka, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Yana bayyana dalilan ziyarar ta cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce ƙasar na fuskantar rikicin cikin gida wanda ba za a iya raina shi ko mayar da shi batun siyasa ba.
Atiku ya yi gargadin cewa gwamnatin Nijeriya na rasa ikon sauke nauyinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
A cewarsa, duk wata gwamnati da ba za ta iya tabbatar da tsaro ba, ta rasa hujjar da za ta samu damar ci gaba da mulki.
Game da tattalin arziki, Atiku ya nuna damuwa kan yadda matsin rayuwa ke ta’azzara a tsakanin al’ummar kasar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma nuna damuwa kan yadda lamarin dimokuraɗiyya a Nijeriya ke tabarbarewa, yana mai gargadin cewa raguwar aminci tsakanin jama’a da shugabanci, gaskiya, da kuma tsarin zaɓe na iya jefa ƙasar cikin barazana.
