DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, October 1, 2026
HomeLabaraiSauye-sauyen Tattalin Arzikin Tinubu ya dora Nijeriya kan hanya madaidaiciya- Hadimin Shugaba...

Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Tinubu ya dora Nijeriya kan hanya madaidaiciya- Hadimin Shugaba Tinubu

Mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan yada labarai da hulda da jama’a, Sunday Dare, ya kare sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kawo, yana mai cewa matakan suna da wahala amma sun zama dole domin hana durkushewar tattalin arzikin kasa.

Dare ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki na Arewa da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar karkashin kungiyar Tinubu Door-to-Door Movement, inda mahalarta suka nuna goyon baya ga sake tsayawar Tinubu takara a zaben 2027.

Ya ce manufofin gwamnatin da suka hada da cire tallafin mai da gyaran tsarin musayar kudaden waje na daga cikin matakan da suka zama wajibi domin dawo da daidaito a harkar kudi da kuma kara karfin gwiwar masu zuba jari.

A cewarsa, duk da wahalhalun da ’yan Nijeriya suka fuskanta a farkon aiwatar da sauye-sauyen, yanzu ana fara ganin alfanun matakan a bangaren tattalin arziki.

Masu shirya taron sun ce manufar gudanar da zaman ita ce kara fahimtar da jama’a kan manufofin gwamnati tare da samar da damar jin ra’ayoyin al’umma kai tsaye daga tushe.

Mai kula da kungiyar PBAT Door-to-Door Movement, Sunday Adekanbi, ya ce taron zai taimaka wajen rage tazara tsakanin gwamnati da jama’a ta hanyar tattaunawa kan aiwatar da manufofi da harkokin mulki.

Sauran wadanda suka gabatar da jawabi sun tattauna kan salon mulkin gwamnatin Tinubu da kuma sauye-sauyen da aka aiwatar, ciki har da ayyukan gine-gine da shirye-shiryen tallafa wa jama’a kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Daya daga cikin masu jawabin, Farfesa Solomon Gushibet daga cibiyar NIPSS da ke Kuru, ya yi bayani kan tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa da kuma amfaninsu a nan gaba.

Shi ma Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na Jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, wanda ya wakilci gwamna Uba Sani, ya ce cire tallafin mai ya taimaka wajen kara kudaden shiga da kuma dawo da zaman lafiya a wasu yankunan jihar da ke fama da matsalolin tsaro.

Mahalarta taron sun bukaci a ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnati domin tabbatar da dorewar ci gaba da zaman lafiyar tattalin arziki a kasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata