DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 30, 2026
HomeLabaraiMajalisar Wakilai ta yaba wa ƙoƙarin sojoji na kawo ƙarshen hare-haren ’yan...

Majalisar Wakilai ta yaba wa ƙoƙarin sojoji na kawo ƙarshen hare-haren ’yan ta’adda a Nijeriya

’Yan Majalisar wakilan Nijeriya sun yi jinjina ga hedikwatar tsaron kasar ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaro, Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede, bisa jajircewar sojoji wajen yaƙi da ’yan ta’adda da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke barazana ga zaman lafiya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yabon ya zo ne yayin da rundunar sojin Nijeriya ke ƙara zafafa ayyukan soji a wurare daban-daban, musamman ƙarƙashin Operation Hadin Kai, Operation Fansan Yamma, Operation Whirl Stroke da Operation Savannah Shield.

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Philip Agbese ne ya bayyana matsayin ’yan majalisar, inda ya ce rundunar sojin Nijeriya ta wuce matakin magana ta fatar baki zuwa aiwatar da hare-haren da ke ƙara matsa lamba kan ƙungiyoyin ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

Agbese, wanda ɗan majalisa ne daga jihar Benue kuma ɗan Jam’iyyar Labour Party, ya ce ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka da kwato makamai na nuna cewa sojoji na ƙara kai farmaki ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka maimakon jiran a kai musu hari.

Ya ce bayanan hedikwatar tsaro sun nuna cewa a cikin watannin Yuli da Agusta, sojoji sun gudanar da jerin ayyuka a sassan Nijeriya, inda suka ce an hallaka ko kawar da ’yan ta’adda da masu tayar da kayar baya 1,487, tare da ceto mutane 777 da aka yi garkuwa da su da kama waɗanda ake zargi 354.

A yayin ayyukan, rundunar ta ce ta kwato bindigogi 91, harsasai 1,331 da kuma na’urorin fashewa 44 IEDs.

A yankin Arewa maso Gabas, sojojin Operation hadin kai sun ci gaba da gudanar da kakkaɓe ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke Arewa maso Gabas musamman a jihohin Borno da Yobe.

Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce a watan Agusta kaɗai, an kawar da ’yan ta’adda 114, an kama mutane 146 da ake zargi, sannan an ceto mutane 60 da aka yi garkuwa da su a ayyukan da aka gudanar a yankin.

A yankin Arewa maso Yamma kuwa, sojojin Operation Fansan Yamma, tare da tallafin rundunar sojin sama, sun ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a Kaduna, Katsina, Sokoto da Zamfara.

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta kuma tare wasu ’yan ta’adda da ke tafiya da dimbin mutanen da suka yi garkuwa da su a yankin Bazama na ƙaramar hukumar Sakaba a jihar Kebbi.

Matakin ya ba fiye da mutane 60 da aka yi garkuwa da su damar tserewa daga hannun masu garkuwar.

Sojoji sun kuma ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Dandume zuwa Damari a Katsina a ranar 17 ga Satumba, yayin da aka ceto wasu uku a ƙaramar hukumar Bakura ta Zamfara ranar 18 ga Satumba.

A ranar 20 ga Satumba, an ceto wasu mutane 17 da aka yi garkuwa da su a yankin Isa-Kwanar da ke jihar Sokoto, yayin da sojoji suka sake ceto ɗaliban jami’a bakwai da aka yi garkuwa da su a hanyar Daye zuwa Malumfashi a Katsina ranar 21 ga Satumba.

Haka kuma, a ranar 24 ga Satumba, sojoji sun ce sun ceto mutane biyar a ƙauyen Sekpore da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta Zamfara, ciki har da Shugaban karamar hukumar Bungudu da aka yi garkuwa da shi.

A yankin Arewa ta Tsakiya, sojojin Operation Whirl Stroke sun ci gaba da ayyuka kan masu garkuwa da mutane da masu safarar makamai a Benue, Kogi, Nasarawa da Taraba.

A ranar 18 ga Satumba, sojoji sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a hanyar Takum zuwa Katsina-Ala a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta Benue.

A Nasarawa kuma, sojoji sun kai samame gidan wani da ake zargi da jagorantar ƙungiyar masu garkuwa da mutane a Bukan Sidi da ke cikin garin Lafia a ranar 19 ga Satumba.

An ce sojojin sun kama wanda ake zargin tare da gano bindiga ƙirar gida, kayan sojan da aka kera irin na rundunar, wata mota mai tsada da kuma kuɗi har Naira 406,200.

Majalisar wakilai ta ce ci gaba da matsin lamba daga sojoji, inganta tattara bayanan sirri, haɗin gwiwar hukumomin tsaro da samar da isassun kayan aiki na iya taimakawa wajen rage barazanar ’yan ta’adda tare da ba al’ummomin da abin ya shafa damar komawa rayuwa ta yau da kullum.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata