DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 30, 2026
HomeLabaraiSojojin Nijeriya sun kama ’yan bindiga 350, sun kuɓutar da mutane 655...

Sojojin Nijeriya sun kama ’yan bindiga 350, sun kuɓutar da mutane 655 a watan Satumba

Sojojin Nijeriya sun ce ’yan ta’adda da masu aikata laifuka 350 sun shiga Komarsu tare da kuɓutar da fararen hula 655 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar cikin watan Satumba na 2026.

Rundunar ta kuma ce dakarunta sun fuskanci jimillar hare-hare 367 a sassa daban-daban na Nijeriya a cikin watan, inda suka ce sun mayar da martani tare da hallaka ’yan ta’adda da masu aikata laifuka 52.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar Michael Onoja shi ya sanar da hakan yayin da yake bayyana nasarorin da rundunar ta samu a fannonin ayyukan tsaro a ranar Laraba.

Ya ce cikin hare-haren 367 da aka kai, rundunar Operation Enduring Peace ce ta kai mafi yawan hare-hare da suka kai 147, sai Operation Fansan Yamma da hare-hare 115.

Onoja ya ce rundunar Operation Whirl Stroke ta kai hare-hare 55, yayin da Operation Hadin Kai ta kai 33.

Ya ƙara da cewa Operation Savannah Shield ta kai hare-hare 13, yayin da Operation Udo Ka OPUK ta samu kai huɗu.

Daraktan ya ce dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa ga hare-haren da aka kai musu, inda suka yi amfani da dabarun yaƙi da ƙarfin soji wajen tunkarar maharan tare da dakile hare-haren.

A cewarsa, a cikin watan Satumba rundunar ta kuma kuɓutar da mutane 655 da aka yi garkuwa da su, yayin da wasu ’yan tawaye 75 suka miƙa wuya ga jami’an tsaro.

Baya ga haka, rundunar ta ce ta kwato makamai 52 da kuma harsasai 2,335 a yayin ayyukan da ta gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.

Hedikwatar tsaron ta kasa ta kuma ce dakarun sun lalata matatun mai guda takwas da ake zargin an yisu ba bisa ka’ida ba, tare da kwato sama da lita 304,822 na man fetur da aka sace.

Manjo Janar Onoja ya ce bayanan ayyukan watan Satumba na nuna ƙudurin rundunar sojin Nijeriya na ci gaba da samar da yanayi mai kyau na tsaro a dukkan wuraren da take gudanar da ayyukanta.

Ya ce ayyukan sojojin sun shafi yaƙi da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a sassan Arewa, da kuma matsalolin garkuwa da mutane, satar man fetur da kuma wasu barazanar tsaro a kudancin ƙasar.

Da yake bayyana sakamakon ayyukan shekarar 2026, Onoja ya ce sojoji sun hallaka ’yan ta’adda da masu aikata laifuka 554, tare da kama wasu 1,333.

Ya ce a cikin wannan lokaci, an kuma kuɓutar da mutane 1,736 da aka yi garkuwa da su, yayin da 333 ’yan tawaye suka miƙa wuya ga hukumomin tsaro.

A cewar rundunar, dakarunta sun kwato makamai 244 da harsasai 8,160 a cikin kwata ta uku, tare da lalata matatun mai 104 da ake gudanarwa ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma, an ce an kwato sama da lita miliyan 1.6 na man fetur da aka sace a cikin watanni uku.

Hedikwatar tsaro ta kasa ta ce ci gaba da ayyukan sojojin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage barazanar ’yan ta’adda, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a sassan Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata