DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 30, 2026
HomeLabaraiTurmutsitsi yayin rabon tallafi ya yi sanadin hallaka mutum uku a gidan...

Turmutsitsi yayin rabon tallafi ya yi sanadin hallaka mutum uku a gidan gwamnatin Neja

Aƙalla mutane uku, wata mata da ’yarta da kuma wata mace, sun mutu, wasu kuma da dama suka jikkata sakamakon turmutsitsi da ya barke a gidan gwamnatin jihar Neja da ke Minna.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, bayan da aka samu rahoton cewa Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya bayar da umarnin raba Naira 10,000 ga matasan da suka taru a gidan gwamnatin domin nuna goyon baya ga gwamnatinsa.

Rahotanni sun ce taron ya samu halartar dimbin matasa da suka taru domin bayyana goyon bayansu ga gwamnatin Bago tare da nuna rashin goyon bayan wani shirin zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a Minna a ranar 1 ga Oktoba.

Sai dai lamarin ya rikide zuwa rudani bayan da jami’an gwamnati suka fara rabon kuɗin, N10,000 ga mutanen da suka taru a wurin.

Rahotannin sun ce fara rabon kuɗin ya haifar da turmutsitsi, wanda ya jikkata mutane da dama inda aka kai wasu daga cikinsu asibiti domin samun agajin gaggawa.

Daga cikin waɗanda aka ruwaito sun mutu akwai Hulaira da ’yarta Dije, waɗanda aka bayyana a matsayin ’yan gudun hijira daga ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Rahoton ya ce Hulaira da Dije sun rasu ne a babban asibitin Minna, bayan da aka kai su can sakamakon raunukan da suka samu a lokacin turmutsitsin.

An kuma ruwaito cewa an binne gawarwakin Hulaira da ’yarta Dije a makabartar Unguwan Daji da ke Minna Larabarnan.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ake ci gaba da fuskantar wasu matsalolin tsaro da na zamantakewa a jihar, ciki har da mutuwar mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne, waɗanda suka mutu a hannun jami’an hukumar tsaro ta NSCDC.

Kafin taron, wasu daga cikin hadiman Gwamna Bago, ciki har da mai ba shi shawara kan hulɗa da kafafen yaɗa labarai, Alfa Kayan Bago, sun yi kira ga matasa su zauna lafiya tare da nisantar shirin zanga-zangar da aka tsara.

Kayan Bago ya ce wasu matasan da ake danganta su da shirin zanga-zangar sun ziyarci Gwamna Bago a gidan gwamnati, inda suka bayyana aniyarsu ta tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Sai dai har zuwa lokacin da rahoton ya fito, rundunar ’yan sandan jihar Neja ba ta tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata