DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaAPC ta tantance Jamil Gwamna gabanin zaben fidda gwanin Gombe

APC ta tantance Jamil Gwamna gabanin zaben fidda gwanin Gombe

Jam’iyyar APC ta tantance Dr. Jamil Isyaku Gwamna domin shiga zaben fidda gwani na gwamnan Jihar Gombe da za a gudanar nan gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa APC ta zabi Jamil Gwamna a matsayin dan takarar sasanci a jihar, duk da cewa wasu masu neman takarar biyu, Sanata Saidu Ahmed Alkali da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, sun nuna rashin amincewa da tsarin.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ibrahim Sani Shawai ya fitar, ya ce an gudanar da tantancewar ne ranar Asabar a Abuja bisa dokokin jam’iyyar da ka’idojin cikin gida na APC.

Kwamitin tantancewar karkashin jagorancin Dr. Benjamin Obi Nwoye ya ce Jamil Gwamna ya cika duk sharuddan da suka dace domin shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Bayan tantancewar, Jamil Gwamna ya yaba wa shugabannin APC bisa gudanar da aikin cikin gaskiya da adalci, yana mai cewa hakan ya kara nuna karfin dimokuradiyyar cikin gida a jam’iyyar.

Ya kuma jaddada kudirinsa na ci gaba da ayyukan ci gaban da gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta fara a jihar.

Dan takarar ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu da gwamna Inuwa Yahaya, yana mai cewa ayyukan da suke yi sun kara wa APC karbuwa a matakin kasa da jiha.

Haka kuma ya bukaci ’ya’yan APC da magoya baya su kasance cikin hadin kai da biyayya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata