Hukumar NDLEA ta kama wasu mutane uku masu bukata ta musamman bisa zargin safarar miyagun kwayoyi a jihohin Anambra da Kwara.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, ya ce jami’an NDLEA sun kama wani mutum mai shekaru 60 mai suna Romanus Nwabara a dajin Akpaka da ke Onitsha dauke da gram 250 na tabar wiwi da aka shirya domin sayarwa.
A wani samame da aka kai a Ogbunike a jihar Anambra, jami’an sun sake kama Amos Kenneth mai shekaru 25 da wasu kwayoyin Tramadol, Diazepam, Exol-5 da kuma tabar wiwi.
A jihar Kwara kuwa, jami’an NDLEA sun kama Usman Salisu a cikin motar haya a Bode Saadu bayan gano kilo 6.3 na tabar wiwi da aka boye a cikin jakar makaranta.
Hukumar ta kuma ce jami’anta sun kai samame wani gida a Lekki Phase 1 da ake zargin ana boye miyagun kwayoyi a ciki, inda suka kwato buhuna 4,000 na wani nau’in tabar wiwi mai suna “Loud” mai nauyin kilo 2,326 da kudinsa ya haura naira biliyan 5.8.
An kuma kama Emmanuel Osita Okeke a Nasarawa da kilo 129 na tabar wiwi, yayin da jami’ai suka tare wata motar fasinja a hanyar Okene zuwa Lokoja suka kwato buhuna 76 na tabar wiwi masu nauyin kilo 766 tare da kama mutane uku.
A Lagos kuwa, jami’an NDLEA sun kai samame wani wajen hada “skuchies” a Ijora Badia inda suka kama mutane biyu tare da kwato lita 270 na hadin miyagun kwayoyi.
Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yabawa jami’an hukumar kan nasarorin da suka samu tare da bukatar su kara kaimi wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi a fadin kasar.
