DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeLabaraiHarin sojin ta sama ya yi sanadiyyar ajalin mutane sama da 100...

Harin sojin ta sama ya yi sanadiyyar ajalin mutane sama da 100 a jihar Zamfara

Rahotanni daga karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara sun ce wani harin jirgin saman sojin Nijeriya da aka kai kasuwar Tumfa ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 117 tare da jikkata wasu da dama.

Mazauna yankin sun ce wadanda abin ya shafa sun hada da ‘yan bindiga da kuma fararen hula.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a ranar Lahadi, ranar da rundunar sojin saman Nijeriya ta kai wani hari kan ‘yan bindiga a yankin Guradnayi kusa da Kusasu a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, inda aka ce mutum 13 fararen hula suka mutu kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

An samu jinkirin bayyana labarin harin na Tumfa ne saboda matsalar hanyoyin sadarwa a yankin. Rahotanni sun ce Tumfa da wasu kauyukan da ke makwabtaka da ita na karkashin ikon kungiyoyin ‘yan bindiga, inda mazauna yankin ke rayuwa tare da su saboda rashin tsaro.

Wani jagoran al’umma mai suna Garba Ibrahim Mashema ya ce har yanzu yana da wahala a tantance adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai kasuwar.

Shi kuma wani mazaunin garin Zurmi mai suna Aliyu Musa, wanda garinsu ke da tazarar kusan kilomita bakwai daga Tumfa, ya ce da yawa daga cikin wadanda suka mutu ‘yan kasuwa ne da masu sayar da abinci, ciki har da ‘yan mata masu sayar da kunu da awara. Ya kiyasta adadin wadanda suka mutu zuwa 117.

Aliyu Musa ya yi zargin cewa watakila jami’an soji sun hangi makamai a cikin kasuwar yayin sintiri ta sama, lamarin da ka iya sa aka kai harin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata