Gwamnan Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Nijeriya Dikko Umaru Radda, ya ce jiharsu a yanzu ta zama abin koyi wajen nazarin yadda ake amfani da haɗin gwiwar al’umma domin magance matsalolin tsaro.
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin da ya ke karɓar baƙuncin jami’an tsaro mahalarta kwas kan harkar tsaro da suka kai ziyarar nazari jihar Katsina.
Tawagar ta ƙunshi mutum 91 da suka haɗa da jami’an koyarwa da gudanarwa, daliban jami’an rundunar sojin ruwa da na sama, tare da mahalarta daga ƙasashen Gambia, Côte d’Ivoire da Liberia.
Sun kai ziyarar ne a ƙarƙashin shirin Environmental Study Tour mai taken “Inganta Haɗin Gwiwar Al’umma Domin Ƙarfafa Tsaro da Cigaban Ƙasa.”
Gwamnan ya ce matsalar tsaro ba abu ba ne da za a warware wa cikin dare ɗaya, yana mai jaddada cewa tana buƙatar cikakken fahimta da kuma tsari mai cike da haɗin kai.
Ya ce irin wannan bincike zai taimaka wajen samar da mafita masu amfani ga ƙasar baki ɗaya.
Radda ya bayyana cewa gwamnatin sa ta rungumi tsarin tsaro na haɗin gwiwar al’umma bayan gano cewa yawan jami’an tsaro bai isa ya magance matsalolin tsaron da ake fuskanta a faɗin ƙasar ba.
“Mun fahimci cewa adadin jami’an soja, ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya bai isa ba, shi ya sa muka rungumi tsarin da ya haɗa al’umma kai tsaye,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa mafi yawan hare-haren tsaro na faruwa ne a ƙauyuka masu nisa inda jami’an tsaro kan ɗauki lokaci kafin isa, lamarin da ya sa aka samar da wata kariya ta farko daga cikin al’umma tare da tattara bayanan sirri.
Gwamnan ya bayyana cewa matsalolin tsaro a Katsina sun fi alaƙa da satar shanu da garkuwa da mutane maimakon ta’addanci mai alaƙa da akida, wanda hakan ya sa haɗin kan jama’a ya zama wajibi.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta kafa rundunar Katsina Community Watch Corps domin taimaka wa jami’an tsaro na gargajiya.
A cewarsa, an ɗauki mambobin rundunar ne ta hanyar tsari mai kyau, sannan sojoji da ‘yan sanda suka horas da su kafin a tura su aiki.
“Sun fi sanin yankunan su kuma suna iya kai dauki cikin sauri. Gudummawar su wajen tattara bayanan sirri da kai martani cikin gaggawa ta taimaka wajen rage matsalar tsaro sosai,” in ji Gwamnan.
Ya ƙara da cewa tsarin ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankuna da dama tare da ba manoma damar komawa gonakinsu.
Gwamna Radda ya kuma bayyana cewa shugabannin gargajiya, malamai, matasa da hukumomin ƙananan hukumomi sun taka muhimmiyar rawa wajen dawo da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da haɗin kai.
