DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeLabaraiMasu shigo da man daga waje sun yi ƙokarin kawo cikas ga...

Masu shigo da man daga waje sun yi ƙokarin kawo cikas ga matatata – Dangote

Attajirin Afirka Aliko Dangote ya ce wasu masu shigo da man fetur a Nijeriya sun yi kokarin dakile aikin matatar man fetur dinsa ta dala biliyan 20.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shugaban Asusun Arzikin Norway, Nicolai Tangen, a shirin “In Good Company” inda ya ce akwai wasu manyan ‘yan kasuwa da ke cin moriyar tsarin tallafin man fetur a kasar.

A cewarsa, tsarin rabon man fetur da gwamnati ke yi a lokacin tallafi ya bai wa wasu tsirarun mutane damar tara biliyoyin naira.

“Saboda tallafin mai, akwai wasu kalilan da ke samun rabon man fetur kuma suna samun biliyoyin naira daga tsarin,” in ji Dangote.

Ya ce irin wadannan mutane ne suka yi kokarin hana aikin matatar saboda suna ganin zai kawo karshen ribar da suke samu daga shigo da man fetur.

Dangote bai ambaci sunayen mutanen ko kamfanonin da yake zargi ba, amma ya jaddada cewa duk da matsin lambar da aka yi, aikin matatar ya samu nasarar kammaluwa.

Matatar Dangote da ke Lekki a jihar Legas na daya daga cikin manyan matatun mai a duniya, kuma ana sa ran za ta rage dogaron Nijeriya kan shigo da man fetur daga kasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata