Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, sun bayyana cewa ingantaccen ilimi, haɗin kan al’umma da hukumomin tsaro, da kuma tarbiyya mai kyau su ne muhimman hanyoyin magance matsalar ƴan bindiga, ta’addanci da sauran barazanar tsaro a Nijeriya.
Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, sun bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da makarantar Kaduna Christian Academy, wata makaranta da aka bai wa al’ummar Kiristoci a jihar Kaduna. Abokan Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Oluwatosin Ajayi, ne suka samar da makarantar. A baya ma irin wannan ƙungiya ta taimaka wajen gina makarantar Musulmai a Danbushiya da ke ƙaramar hukumar Chikun.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ce nasarar yaƙi da rashin tsaro ba ta ta’allaka ga amfani da sojoji da makamai kawai ba. Ya ce ilimi na daga cikin manyan hanyoyin yaƙi da jahilci, da kuma ra’ayoyin masu tsattsauran ra’ayi da ke haddasa matsalolin tsaro.
Ya ce mutane da dama na kallon tsaron ƙasa ta fuskar sojoji, jiragen yaƙi da tattara bayanan sirri kawai, amma a zahiri ilimi ne ginshiƙin zaman lafiya mai ɗorewa. A cewarsa, makarantar da aka buɗe wata muhimmiyar gudunmawa ce wajen gina al’umma mai ilimi da rage yiwuwar fadawar matasa cikin miyagun ayyuka.
Ministan ya yabawa Hukumar DSS bisa yadda take haɗa ayyukan tsaro da shirye-shiryen ci gaban al’umma. Ya ce al’umma masu ilimi sun fi sauƙin fahimtar hatsarin aikata laifuka kuma suna taka rawa wajen ci gaban ƙasa. Haka kuma ya bukaci iyaye su mayar da hankali wajen bai wa ‘ya’yansu ilimi, yana mai jaddada cewa kowane yaro na da damar samun nasara idan aka ba shi ilimi da goyon baya.
Christopher Musa ya kuma yaba da ci gaban da aka samu a fannin tsaro a jihar Kaduna, inda ya danganta hakan da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar da kuma ƙananan hukumomi. Ya yabawa Gwamna Uba Sani bisa kokarinsa na inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a jihar.
Ministan ya kuma yi kira ga al’umma da su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan masu aikata laifuka. Ya ce galibin ƴan ta’adda da ƴan bindiga na samun bayanai da tallafi daga wasu mutane a cikin al’umma, saboda haka jami’an tsaro ba za su iya cin nasara su kaɗai ba tare da haɗin kan jama’a ba.
A madadin Gwamna Uba Sani, Babban Lauyan Jihar Kaduna kuma Kwamishinan Shari’a, James Kanyip, ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ƙoƙarin faɗaɗa damar samun ilimi mai inganci. Ya bayyana ƙaddamar da makarantar a matsayin wata alama ta fata da ci gaba ga matasa masu tasowa.
Shi kuwa Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta CAN na jihohin Arewa 19 da Abuja, Fasto Joseph Hayab, ya ce an samar da makarantar ne saboda muhimmancin ilimi wajen rage talauci, rashin tsaro da sauran matsalolin zamantakewa. Ya ce makarantar za ta mayar da hankali wajen gina tarbiyya, shugabanci da kyawawan ɗabi’u tare da ilimin zamani.
A nasa jawabin, Limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, Sheikh Suleiman Adam, ya yabawa Darakta Janar na DSS bisa tallafa wa al’ummomin Musulmi da Kirista ta hanyar samar da irin waɗannan makarantu, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabambantan addinai.
