Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabbin matakai domin ƙarfafa kula da kuɗaɗen gwamnati, inda ta rage iyakar kuɗaɗen gudanar da aiki da ministoci za su iya karɓa zuwa N700,000 tare da tsaurara dokokin kashe kuɗaɗen jama’a.
Sabbin matakan suna ƙunshe ne a cikin Takardar Umarnin Kuɗaɗen Gudanar da Aiki ta shekarar 2026 da Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Mista Taiwo Oyedele, ya sanya wa hannu, sannan Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya fitar da ita ranar 3 ga Yuni, 2026.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sabuwar dokar ta tanadi cewa ministoci ba za su iya karɓar fiye da N700,000 domin gudanar da ayyukan ofis na yau da kullum ba. Haka kuma sakatarorin ma’aikatu da daraktoci janar za su iya karɓar N500,000, yayin da daraktoci da shugabannin sassa za su iya karɓar N300,000. Shugabannin ofisoshi a jihohi da sauran jami’an da aka ba izini kuwa ba za su wuce N100,000 ba.
Takardar ta kuma ce za a iya dawo da irin waɗannan kuɗaɗe sau ɗaya kacal a cikin kowane wata uku, kuma ba za a wuce sau biyu ba sai idan akwai wata buƙata ta musamman. Haka kuma gwamnati ta umurci dukkan hukumomi da ma’aikatu cewa duk wani sayen kaya ko hidima da ya haura Naira miliyan ɗaya dole ne a bi tsarin bayar da kwangila kamar yadda doka ta tanada.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta umarci dukkan ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati su gabatar da bayanan yadda aka kashe kuɗaɗen gudanar da aiki na shekarar 2025 tare da jerin sunayen jami’an da za su riƙe irin waɗannan kuɗaɗe a shekarar 2026 cikin kwanaki 30.
Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi, ya yi gargadin cewa za a ci gaba da gudanar da bincike a kan yadda ake amfani da waɗannan kuɗaɗe, kuma duk jami’in da ya karya dokokin zai fuskanci hukunci, har da cire masa ikon kula da irin waɗannan kuɗaɗe.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na ƙarfafa gaskiya da riƙon amana wajen kashe kuɗaɗen jama’a, bayan rahotanni da dama sun nuna matsalolin rashin bin ƙa’idoji da jinkirin gabatar da bayanan yadda aka kashe wasu kuɗaɗen gwamnati.
