DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiAtiku ya nemi a kuɓutar da sauran waɗanda aka sace bayan ceto...

Atiku ya nemi a kuɓutar da sauran waɗanda aka sace bayan ceto mutum 360 a Borno

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yaba da nasarar da jami’an tsaro suka samu wajen kuɓutar da mutum 360 da ‘yan ta’adda suka sace a Ngoshe da ke Jihar Borno, tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen ceto sauran mutanen da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, dakarun rundunar Operation HADIN KAI ne suka gudanar da aikin ceton bayan sun kuɓutar da mutanen daga tsaunukan Mandara, wani yanki da aka sani da zama mafakar ‘yan ta’adda a kudancin Jihar Borno.

Sace mutanen ya biyo bayan harin da mayaƙan Boko Haram suka kai wa sansanin sojoji da ke Ngoshe a watan Maris.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce ya yi matuƙar farin ciki da samun labarin ceto mutanen, yana mai cewa hakan ya kawo ƙarshen wahalar da suka sha tare da rage damuwar iyalansu da suka shafe watanni suna cikin fargaba.

Ya yabawa rundunar sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da suka taka rawa wajen gudanar da aikin ceton cikin nasara. Atiku ya ce yana da yakinin cewa idan aka samar wa jami’an tsaro kayan aiki da jagoranci nagari, za su iya kawo ƙarshen rikicin ta’addanci da ya shafe kusan shekaru 20 yana addabar ƙasar.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce duk da wannan nasara, akwai buƙatar ƙara ƙoƙari domin ceto kusan ɗalibai da malamai 100 da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire ta Jihar Oyo da kuma Mussa da ke Jihar Borno, da kuma sauran mutanen da ke hannun ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a faɗin Nijeriya.

Atiku ya kuma yi kira da a sake fasalin tsarin tsaron ƙasar ta yadda za a fi mayar da hankali kan tattara bayanan sirri, amfani da fasaha da kuma dakile hare-hare kafin su faru. A cewarsa, hakan ne zai taimaka wajen rage hare-haren ta’addanci da matsalar ‘yan bindiga a ƙasar.

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana aikin ceton a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan kuɓutar da mutane da aka yi a yankin Arewa maso Gabas cikin ‘yan shekarun nan. Ta ce nasarar ta samu ne bayan makonni na tattara bayanan sirri, sa ido a ɓoye da kuma tsara yadda za a gudanar da samamen.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata