Amurka ta shawarci ’yan Nijeriya su kiyaye dokokin shige da fice domin samun bizar shiga kasar
Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya bukaci ’yan Nijeriya da ke tafiya zuwa kasar su kiyaye dokokin shige da fice tare da bin sharuddan da ke kunshe a cikin biza, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kare damar zuwa kasar a nan gaba.
A wata sanarwa da Ofishin Jakadancin ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, ya shawarci masu zuwa Amurka domin karatu, aiki ko yawon bude ido da su tabbatar sun bi ka’idojin bizar su, tare da kauce wa wuce wa’adin zaman da aka ba su a kasar.
