Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan amincewa da ƙarin albashin jami’an rundunar sojin Nijeriya da tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin 100, yana mai cewa matakin zai inganta walwalar sojoji tare da ƙara musu ƙaimi a yaƙin da suke yi da matsalolin tsaro.
Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa Ministan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Leah Katung-Babatunde, ta fitar a ranar Laraba. Ya ce sabon tsarin karin albashin ya nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na bai wa jami’an da ke kan gaba wajen kare ƙasa kulawar da ta dace.
Ministan ya ce, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake nuna jajircewa da tausayi ga jarumai maza da mata da ke sadaukar da rayuwarsu domin kare zaman lafiya da martabar ƙasar nan.”
Ya ƙara da cewa ƙara kuɗin albashin ma’aikatan rundunar daga N660bn zuwa N924bn ya tabbatar da cewa gwamnatin ta mayar da walwalar sojoji a matsayin abin fifiko.
A cewarsa, karin albashin zai rage matsin tattalin arzikin da jami’an soja ke fuskanta, tare da ƙarfafa ayyukan da suke gudanarwa a yankunan da ake fama da matsalar tsaro. Ya ce hakan zai taimaka wa sojojin da ke yaƙi da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas, da masu yaƙi da ‘yan bindiga, satar ɗanyen mai da masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na ƙasar.
“A madadin rundunar tsaro baki ɗaya, muna tabbatar wa Shugaban Ƙasa da ‘yan Nijeriya cewa za mu mayar da wannan karamci da ƙarin jajircewa, bin doka da kuma inganta ayyukanmu,” in ji Ministan.
Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya kuma buƙaci jami’an soja su ɗauki sabon tsarin albashin a matsayin sabon kira na ƙara himma wajen yaƙi da matsalolin tsaro, kare rayuka da dukiyoyin al’umma, da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
Ministan ya sake jaddada cewa ma’aikatar tsaro za ta ci gaba da mara wa gwamnatin Shugaba Tinubu baya wajen sabunta kayan aikin soja, ƙarfafa amfani da fasaha da kuma inganta walwalar jami’an soja da iyalansu.
A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya sanar da amincewa da karin albashin, yana mai cewa matakin na daga cikin hanyoyin girmama sadaukarwar da jami’an soja ke yi wajen yaƙi da ta’addanci, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Sabon tsarin albashin zai fara aiki daga 1 ga Satumba, 2026, kuma zai shafi kusan jami’an soja 250,000 na Rundunar Sojin Ƙasa, Rundunar Ruwa da Rundunar Sojin Sama.
A ƙarƙashin sabon tsarin, sojoji daga mukamin Private zuwa Staff Sergeant za su samu karin albashi na kashi 80 cikin 100, jami’ai daga Warrant Officer zuwa Colonel za su samu kashi 50 cikin 100, yayin da manyan hafsoshi daga Brigadier-General zuwa General za su samu kashi 30 cikin 100.
