DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaSama da malamai 200 sun bar jami’ar Kaduna saboda rashin kyawun yanayin...

Sama da malamai 200 sun bar jami’ar Kaduna saboda rashin kyawun yanayin aiki – ASUU

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya, ASUU, reshen Jami’ar jihar Kaduna (KASU), ta ce sama da malamai 200 sun bar jami’ar sakamakon rashin kyawun yanayin aiki da kuma gazawar jami’ar wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta kulla da ASUU a shekarar 2025.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban ASUU na jami’ar ta Kaduna (KASU), Dr Abubakar Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Kaduna ranar Litinin.

Abdullahi ya ce yarjejeniyar FGN-ASUU ta shekarar 2025, wadda ta tanadi inganta albashi da sauran sharuddan aikin malaman jami’o’in Nijeriya, ta fara aiki tun daga watan Janairun 2026, amma har yanzu ba a fara aiwatar da ita a KASU ba.

Saboda haka, kungiyar ta bai wa mahukuntan jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin makonni biyu su fara cikakken aiwatar da yarjejeniyar tare da sanya ta cikin tsarin dokokin jami’ar.

ASUU ta yi gargadin cewa idan wa’adin ya kare ba tare da an dauki matakin da ya dace ba, za ta fara yajin aikin gama-gari, cikakke kuma ba tare da kayyade lokacin da za a dakatar da shi ba.

Shugaban kungiyar ya ce ASUU-KASU ta rubuta wasiku da dama zuwa ga mahukuntan jami’ar, majalisar gudanarwarta da kuma mai kula da jami’ar, Gwamna Uba Sani, tana neman a aiwatar da yarjejeniyar kamar yadda dokar da ta kafa jami’ar ta tanada.

Ya ce kungiyar ta kuma tuntubi masu ruwa da tsaki a ciki da wajen jihar domin neman mafita da kuma kauce wa duk wani rikicin masana’antu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da ayyukan jami’ar.

Abdullahi ya nuna damuwa kan yadda sama da watanni takwas bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, jami’ar har yanzu ba ta fara aiwatar da ita ba.

A cewarsa, wannan jinkiri ya sanya malaman KASU cikin wadanda ake biyan mafi karancin albashi a tsakanin ma’aikatan jami’o’in kasar, duk da cewa jami’ar a baya ta yi suna wajen kula da jin dadin ma’aikatanta.

Ya kuma yi gargadin cewa ci gaba da jinkirin zai haifar da tarin bashin albashi da zai fara daga watan Janairun 2026.

Shugaban ASUU-KASU ya danganta barin jami’ar da kwararrun malamai, ciki har da furofesoshi da sauran manyan malamai, da rashin isasshen albashi da yanayin aiki mara kyau.

Ya ce mafi yawan malaman da suka bar jami’ar sun samu guraben aiki a wasu jami’o’i da ke cikin Kaduna da sauran jihohin Najeriya.

Daga cikin sauran matsalolin da kungiyar ta ce suna damun malaman KASU akwai batun cin gashin kan jami’ar, yawan aikin da ake dora wa malamai, bashin karin girma, hakkokin mutanen da suka rasu, inshorar rayuwar rukuni, tallafin albashi na kashi 25 da 35 cikin 100, da kuma kudaden fansho da ba a tura ba.

ASUU ta bukaci mahukuntan jami’ar da sauran hukumomin da abin ya shafa su dauki matakan gaggawa wajen warware matsalolin domin dakile karin ficewar malamai da kuma kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a jami’ar.

Kungiyar ta kuma bukaci a biya dukkan bashin albashin malaman da ya taru tun daga Janairun 2026, tare da inganta albashi da samar da yanayin aiki mai kyau.

Abdullahi ya ce musamman ya kamata a dauki matakan gaggawa domin dakatar da ficewar furofesoshi, masu digirin digirgir da sauran kwararrun malamai, domin sake gina irin wannan kwarewa a jami’a na iya daukar shekaru masu yawa.

Ya ce idan aka aiwatar da bukatun kungiyar yadda ya kamata, hakan zai taimaka wajen rike malaman da suke jami’ar tare da karfafa gwiwar sauran malamai su ci gaba da aiki a KASU.

A halin yanzu, mahukuntan Jami’ar Jihar Kaduna ba su fitar da martani kan zarge-zargen da bukatun ASUU ba.

Haka kuma, kwamishinan yada labarai na jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya yi alkawarin mayar da martani bayan an tuntube shi, amma har zuwa lokacin da rahoton ya kammala ba a samu wani karin bayani daga gare shi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata