Hukumar yaƙi da rashawa ta Nijeriya, EFCC, ta fara bincike kan wani mutum mai suna Haruna Yusuf, bayan hukumar kwastam ta Nijeriya ta kama makudan kudaden kasashen waje da ba a bayyana ba a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano.
Jimillar kudaden da aka kama sun kai dalar Amurka 73,000, fam 15,957 da kuma Riyal din Saudiyya 827,800. An kama kudaden ne yayin aikin tantance fasinjoji da jami’an kwastam suka gudanar tsakanin 8 zuwa 12 ga watan Agustan 2026.
Mukaddashin Kwanturolan hukumar Kwastam ta Kano da Jigawa, Deputy Comptroller U.U. Adamu, ne ya mika wanda ake zargin da kudaden da aka kwato ga EFCC domin gudanar da cikakken bincike da daukar matakin da ya dace.
A cewar Adamu, kamen farko ya faru ne a ranar 8 ga watan Agusta da misalin karfe 2:20 na rana, lokacin da jami’an kwastam ke duba kayan fasinjoji a filin jirgin.
Gidan talabijin na TVC News ya ruwaito shi ya ce jami’an sun gano wani akwati da kamfanin jirgin Saudi Air ya kawo ba tare da mai shi ba, inda aka gano Riyal din Saudiyya 827,800 da kuma dalar Amurka 53,300.
Adamu ya bayyana cewa an boye kudaden ne a cikin takalma da ke cikin kayan.
A ranar 12 ga watan Agusta kuma, jami’an kwastam sun sake kama wasu kudade yayin da suke tantance kayan Haruna Yusuf, wanda ya shigo kasar da jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET941.
A wannan karon, an gano dalar Amurka 20,000 da fam 15,957 da aka boye a cikin takalman wasanni.
Hukumar ta ce an gano kudaden ne bayan amfani da fasahar Non-Intrusive Inspection Technology wajen kara binciken kayan.
Bayan gano kudaden, jami’an kwastam sun mika Haruna Yusuf tare da kudaden da aka kwato ga EFCC domin gudanar da bincike kan yadda aka shigo da kudaden kasar da kuma dalilin da ya sa ba a bayyana su ba.
Adamu ya ce matakin ya yi daidai da tanadin sashe na 4(f) na dokar Nigeria Customs Service Act ta shekarar 2023, wadda ta bai wa hukumar damar hada kai da sauran hukumomin kula da iyakokin kasa.
Ya ce kamen ya nuna yadda jami’an kwastam ke kara kaimi wajen gano safarar kudaden kasashen waje da ba a bayyana ba, musamman wadanda suka haura iyakar adadin da doka ta tanada.
A nasa bangaren, mukaddashin daraktan shiyyar EFCC ta Kano, ACE1 Friday S. Ebelo, wanda ya karbi wanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato a madadin shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yaba wa hukumar kwastam bisa hadin kai.
Ebelo ya ce hukumomin tsaro da kula da iyakokin kasar na bukatar ci gaba da taka tsantsan a dukkan wuraren shige da ficen mutane domin dakile safarar kudade ba bisa ka’ida ba.
Ya jaddada cewa rashin bayyana makudan kudaden da mutum ke dauke da su, ko makamancinsu a kudaden kasashen waje, na iya zama karya dokar Money Laundering (Prevention and Prohibition) Act ta shekarar 2022.
Sai dai EFCC ta bayyana cewa mutum ba zai fuskanci hukunci saboda kawai ya bayyana kudaden da yake dauke da su ba.
Ebelo ya bukaci matafiya da su rika bin dokokin Nijeriya na bayyana kudaden da suke dauke da su, yana mai cewa bayyana kudin ba yana nufin za a kwace shi ba ne.
Ya ce hukumomin gwamnati ba sa hana ‘yan Nijeriya yin kasuwanci ko safarar kudade bisa ka’ida, amma dole ne a bi dokokin da aka gindaya domin tabbatar da gaskiya da tsaron tsarin hada-hadar kudade ta kasar.
